Home General Najeriya ta fara sayar da ɗanyen mai da kuɗin naira

Najeriya ta fara sayar da ɗanyen mai da kuɗin naira

Old Naira

Gwamnatin Najeriya ta ce ƙasar ta fara sayar da ɗanyen mai da tataccen mai da kuɗin ƙasar wato naira.

Ministan kuɗi da tattalin arzikin na ƙasar, Wale Edun ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ma’aikatar kuɗin ƙasar, ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar.

Sanarwar ta ce an fara sayar da ɗanyen man da kuɗin naira ne tun daga ranar ɗaya ga watan Okotoban da muke ciki.

Ministan ya ce hakan na daga cikin matakin da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka da ake sa ran zai haɓa tattalin arzikin ƙasar da ci gaba da zaman lafiya da dogaro da kai.

Mista Edun ya ce Najeriya za ta ci gaba da bin matakan da suka dace, lura da halin da kasuwannin ɗanyen a duniya ke ciki wajen ciyar da ƙasar gaba.

Matakin na zuwa ne mako tara bayan majalisar zartarwar ƙasar ta amince da ƙudurin Shugaba Tinubu na umartar kamfanin NNPCL ta sayar wa matatar mai ta Dangote da sauran matatun cikin gida ɗanyen mai da kuɗin ƙasar wato naira.

Masu sharhi dai naganin matakin sayar da man da naira maimakon dala zai age farashin kuɗin ƙasar waje a ƙasa, lamarin da suke ganin zai karya farashin dala tare da rage hauhawar farashi a ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp