Hukumomi a Najeriya sun ce sun tsamo aƙalla gawarwaki 141 daga cikin mutanen da kwale-kwale ya kife da su ranar Talata a kogin Niger.
Kawo yanzu akwai ragowar mutum 52 da ba a gani ba, waɗanda ake fargabar cewa sun mutu.
Kwale-kwale ta tashi ne daga ƙauyen Gwajibo Mudi, na ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara ɗauke da fasinjoji aƙalla 300 da ke kan hanyarsu ta zuwa maulidi a garin Gwajibo na jihar Niger mai maƙwabtaka.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Jirgin ya kife ne da fasinjoji fiye da 150 galibinsu mata da ƙananan yara, lamarin da ya jefa al’ummar yankin da dama cikin mawuyacin hali da fargaba.
Tuni dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da bayar da umarnin gudanar da bincike domin gano musabbain hatsarin.
Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarni ga jami’ai su tabbatar masu tuƙa kwale-kwalen ba su saɓa dokar haramcin tafiye-tafiye cikin dare.












