Rahotannin daga Nigeriya na bayyana cewa farashin litar mai ya tashi zuwa Naira 1, 030 daga Naira 897 a gidajen mai na kamfanin NNPC a birnin tarayya Abuja a yau Laraba.
Read Also:
Lamarin na baya bayannan ya faru ne bayan NNPC ya yanke shawarar fita daga yarjejeniyar siyan mai da matatar mai ta Dangote.
Hakan na nufin dai, NNPC ba zai ci gaba da zama mai siyan man shi kadai daga Dangote ba.
ko da yake tun kafin kamfanin na NNPCL ya ayyana kara farashin man fetur tuni ake sayar da man a farashin 1,100, wasu gidajen man kan sayar a kan farashin 1030.