Hukumar lura da shige da fice ta Nijeriya NIS ta bukaci jami’anta da su sake zage dantse gami da inganta ayyukan su.
Shugabar hukumar CSI Kemi Nanna Nandap ce ta bayyana hakan yayin taron bikin daga likkafar jami’an hukumar 450 a shalkwatar hukumar dake jihar Kano.
CSI Nandap wadda ta sami wakilcin shugaban hukumar reshen jihar Kano Ibrahim Muhammad Abubakar lafiya ta bayyana muhimmanci Karin girman gami da sake inganta ayyukan hukumar ga jami’an
Abubakar lafiya ya kara da cewa hukumar ta yi wannan Karin girma ne ga Jami’an saboda hazaka da mayar da hankulansu akan aiki, ba wai dan sun fi kowa bane.
Read Also:
“Wannan Karin girma muka fada musu akan cewa, bawai ko sun fi wasu bane saboda hazakar su ne da kuma kwarewar su a wurin aiki, da kuma suka ci jarrabawa shine Allah ya basu wannan matsayin da yanzu suke kai”
“Muna yi musu murna, muna kuma jan hankalin su da su sake daure damararsu, kasancewar akwai Jan aiki a gabansu a wannan ma’aikata ta shige da fice.
Haka kuma shugaban hukumar ya sake zaburar da jami’an hukumar wajen sanya idanu, don magance harkokin safarar mutane dake addabar nahiyar Afirka da ma kasa baki daya.
Inda ya ce hukumar ta shirya tsaf domin sake fadada ayyukanta a kananan hukumomin jihar Kano 44 don kawo karshen wannan matsala.
“Yanzu haka muna da wani shiri da muke jiran umarni daga sama, domin fara wani aiki kafa shingen bincike a dukkanin mashigar jihar kano da ko wacce kusurwa”
Yace sun dauki wannan mataki domin kada ma wadanda ake safarar a sami damar fita ko shigo da jihar Kano.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 14 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 55 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com