Ku marawa Tinubu baya domin ya cimma burin sa – APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta shaida wa ‘yan adawa da su “binne tunanin sauya manufofin da gwamnatin shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ke jagoranta, su marawa gwamnati baya wajen ganin ta cimma burin Shugaban kasa.

Jam’iyyar ta kuma yi watsi da ikirarin da ‘yan adawa suka yi na cewa ta tafka magudi a zaben gwamnan jihar Edo da aka yi ranar 21 ga watan Satumba a wani bangare na shirin kafa tsarin jam’iyya daya da mulkin kama-karya a kasar.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya yi zargin cewa jam’iyyar APC ta yi magudi a zaben Edo domin cimma shirinta na mayar da Najeriya kasa mai jam’iyya daya.

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan taron kwamitin amintattun jami’iyyar, da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa da ke Abuja, shugaban kwamitin, Sanata Adolphus Wabara, ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar zamantakewa da tattalin arzikin kasar, wanda ya dora alhakin hakan kan manufofin gwamnatin APC.

Sai dai da, yake mayar da martani kan zargin a ranar Juma’a, Daraktan Yada Labarai na jam’iyyar APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida wa Aminiya a wata tattaunawa ta wayar tarho cewa jam’iyya mai mulki ba ta da niyyar kawo cikas ga dimokradiyya.

Ibrahim ya ce, “Jam’iyyar APC a matsayinta na jam’iyya mai mulki ba ta da niyyar yi wa kasar nan duk wani abu da zai cutar da dimokradiyyar ta.

APC jam’iyya ce ta ci gaba; jam’iyya ce da ta fito domin kawo sauye-sauye da za su kawo wa al’umma ribar dimokuradiyya. Dimokuradiyya tana da fa’ida ne kawai idan aka samu adawa, amma adawar su zama mai ma’ana, ba barna ba.

“Kasar nan ta yi ta zubar da jini sosai a karkashin shugabancin PDP; sun yi wa kasar zagon kasa. Don haka ’yan Najeriya har yanzu suna kallo sun fara fahimtar ma’anar canji.”

Ya bukaci ‘yan adawa da su yi watsi da tunanin koma-bayan siyasa tare da marawa gwamnati baya.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 6 hours 34 minutes 39 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 8 hours 16 minutes 4 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com