Shugaba Bola Tinubu ya yi tir da yadda aka ci zarafin tawagar Super Eagles ta Najeriya a filin jirgin sama na kasar Libya, yana mai kira ga Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika (CAF) da ta gudanar da cikakken bincike a kai.
Rahotanni sun nuna cewa an sanya ƴan wasan cikin mawuyacin hali, lamarin da ya tilasta musu janyewa daga wasan da aka shirya yi a ranar Talata, kamar yanda Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta tabbatar.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bukaci Kwamitin Ladabtarwa na CAF da ya binciki wannan al’amari tare da hukunta wadanda suka karya dokokin CAF.
Ya jaddada cewa matakan da za a dauka ya zama darasi domin hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
Read Also:
Da yake magana kan yanda aka dauki mataki cikin hanzari, Shugaban ya yaba wa Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje da Ma’aikatar Bunƙasa Wasanni ta Tarayya bisa hadin gwiwar da suka yi, wanda ya tabbatar da dawowar tawagar Super Eagles lafiya.
Wannan ba shi ne karo na farko da aka fuskanci matsala kan tawagogin kwallon kafa na Najeriya a kasashen waje ba.
A shekarar 2019, Super Falcons sun sha irin wannan cin zarafi a kasar Aljeriya, wanda ya sa aka fara tashin hankali kan yanda ake mu’amala da tawagogin kwallon kafa na Afrika a wasannin kasa da kasa.
Duk da wannan matsala da aka samu, Shugaba Tinubu ya jinjinawa Super Eagles bisa jarumtar da suka nuna, inda ya bayyana muhimmancin kwallon kafa a matsayin wata hanya ta hadin kai ga kasa.
Ya kuma yi kira ga hukumomin kwallon kafa da masu sha’awar wasan da su haɗa kai wajen tabbatar da adalci da kuma ganin cewa tawagogin suna samun kima da mutunci a duk inda suka je.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 6 hours 13 minutes 45 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 7 hours 55 minutes 10 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com