Gwamnatin Najeriya da ƴan ƙwadago sun tashi taro babu matsaya kan tsadar rayuwa

Ba a cim ma matsaya ba a taron tattaunawa tsakanin haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin Najeriya game da tsadar rayuwa a ƙasar da ƙarin farashin mai ya haifar.

Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito shugabannin ƙungiyar ma’aikata ta NLC da ta ‘yankasuwa TUC sun gana da wakilan gwamnatin tarayya a ofishin sakataren gwamnati da ke Abuja ranar Alhamis.

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris, ya shaida wa manema labarai a ƙarshen taron cewa taron alama ce da ke nuna yadda gwamnati ta mayar da hankali wajen tattaunawa da ƴan ƙwadago a kan batun.

Sai dai kuma ministan ya ƙi faɗar abubuwan da aka tattauna a wajen taron, yana mai cewa gwamnati ba za ta zura ido har sai abubuwa sun lalace ba sannan ta gana da ƙungiyoyin ƙwadagon.

“An tattauna abubuwa da dama amma kamar yadda na faɗa tun farko, har yanzu ana cikin sasanci ne, kuma wannan harka ce da ba za a iya gamawa a zama ɗaya ba, kuma kawo yanzu ba mu cim ma wani abu da za a iya faɗa wa ƴan Najeriya ba,” in ji shi.

Ƴan Najeriya da dama sun bayyana rashin jin daɗinsu kan ƙarin farashin man fetur da aka yi kwanan nan a ƙasar, da kuma tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 15 hours 20 minutes 18 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 1 minute 43 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com