Bankin Duniya ya yi gargaɗin cewa muddin gwamnatin tarayya ta janye tsare-tsaren tattalin arziki da ta fara, to hakan zai iya janyo babbar cikas ga Najeriya.
Babban wakilin bankin a Najeriya, Dr Ndiame Diop, shi ya yi wannan gargaɗi ranar Alhamis a Abuja yayin kaddamar da wani rahoto kan ‘Cigaban Najeriya da kuma ɗorewarta’ a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsaloli.
Diop ya ce dole ne a ɓullo da tsare-tsaren domin ɗorewar Najeriya, duk da cewa za su janyo tsadar rayuwa da kuma wahalhalu ga ƴan ƙasar.
“Janye waɗannan tsare-tsare zai jefa Najeriya cikin barazana da kuma tawayar tattalin arziki,” in ji Diop.
Ya ce ƙarin kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ta samu a watannin farko na wannan shekara ya faru ne sakamakon cire tallafin man fetur da na kuma na canjin kuɗin waje, inda ya ce hakan ya nuna dole ne a ci gaba da tsare-tsaren.
Tun a lokacin rantsuwar kama aiki ne, shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur, abin da ya jefa ƴan Najeriya da dama cikin kunci da wahalhalu musamman ma masu karamin karfi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 41 minutes 10 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 22 minutes 35 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com