Bankin duniya ya fitar da rahoton ci gaban Najeriya, inda a ciki ya ce sama da mutum miliyan 129 ne suke zaune cikin talauci a ƙasar.
A rahoton wanda bankin ya fitar jiya Alhamis a Abuja, ya nuna hauhawan farashin kayayyaki ne ya jefa miliyoyin ƴan ƙasar a cikin yunwa.
Bankin ya ce sama da mutum miliyan 129, ya nuna ƴan ƙasar masu fama da talauci ya ƙaru ne daga kashi 40.1 a shekarar 2018 zuwa kashi 56 a shekarar 2024.
Rahoton ya ƙara da cewa a shekarar 2023 mutum miliyan 115 ne suke fama da talauci, wanda hakan ke nufin an samu ƙarin mutum miliyan 14 a bana.
PRNigeria Hausa