Majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomi kamar yadda aka tsara a ranar Asabar 26 ga watan Oktoba, 2024, duk da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na hana hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC gudanar da zaben.
Wannan matsaya ta biyo bayan hukuncin da mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yanke a ranar Talata,
Kotu tace wadanda aka bawa mukamin shugabannin hukumar basu cancanta saboda sun kasance magoya bayan jamiyyar NNPP mai mulkin Kano, dan haka kotun tace wadannan mutane basu da damar gudanar da zaben Ƙananan.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci gaba da gudanar da zaben, ko da kuwa hukumomin tsaro irin na ‘yan sanda ba sa iya ba da kariya.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya soki hukuncin kotun, yana mai cewa ya sabawa umarnin da mai shari’a Nura Ma’aji ya bayar a baya, wanda ya haramtawa jam’iyyun siyasa 19 ciki har da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kalubalantar zabe.
“Hukuncin da kotun tarayya ta yanke na tsige shugaban KANSIEC ya ci karo da hukuncin da Mai shari’a Ma’aji ya yanke na hana jam’iyyun siyasa kutsawa cikin harkokin zabe,” in ji Dala.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 8 minutes 44 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 15 hours 50 minutes 9 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com