Kungiyar tuntubar juna ta dattawan arewacin Najeriya, ACF ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren wutar lantarki a daidai lokacin da yankin arewacin ƙasar ke ci gaba da kasancewa cikin duhu sakamakon rashin wuta.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na ƙungiyar, Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ta yi zargin cewa dagan-gan gwamnati ta banzatar da harkar lantarki a yankin domin ƙara jefa harkokin kasuwanci cikin matsi.
ACF ta bayyana mamakin cewa me ya sa arewa wadda ke samar da wutar lantarki mai yawa a ƙasar, amma kuma a ke kasawa a ba ta kaɗan.
“Cikin mako ɗaya da ya gabata, sassan jihohin arewacin Najeriya da dama na fuskantar matsalar rashin wutar lantarki, abin da ya janyo harkokin kasuwanci da na yau da kullum suka kusa durkushewa, ga kuma ƙaruwar ɓacin-rai tsakanin al’umma,” in ji ƙungiyar.
ACF ta ce abin yana tayar da hankali matuka duba da irin sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki a Najeriya (TCN) ya fitar cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar saboda matsalolin tsaro da ake fama da su.
Ta ce bai kamata a ce jihar Legas kaɗai tana da ƙananan tashoshin samar da lantarki har guda takwas ba yayin da ɗaukacin jihohin arewa, waɗanda ke da sama da rabin al’ummar Najeriya ke da tashoshi guda uku kaɗai a Jos da Kaduna da kuma Kano.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa lamarin babbar barazana ce ga tsaron ƙasar.
Don haka ta yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da abin ya shafa da su gaggauta ayyana dokar ta-ɓaci kan matslar ta rashin lantarki, kafin matsalar ra rikiɗe zuwa tashin hankali.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 34 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 16 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com