Gwamnatin jihar kano ta bukaci al’ummar jihar da su fito dumin yi musu gwajin hawan jini, wannan dai na matsayin wani bagare na fara aiwatar da Shirin Gangamin yin gwajin ga Mutane Miliyan Goma a faɗin Nijeriya,
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ya aikewa PRNigeriya a ranar laraba mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Oktoban 2024.
sanarwar ta ce Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi wannan kira a ranar Litinin yayin fara aiwatar da shirin a harabar Hukumar Samar da Magunguna da Kayayyaki ta Jiha (DMCSA).
Shirin Gangamin Mutane Miliyan Goma ya mayar da hankali ne ga cututtuka marasa yaɗuwa, musamman hawan jini da ciwon siga, waɗanda ke taka rawa sosai wajen haifar da cututtuka da mace-mace a Najeriya, da ya sanya Zauren Kwamishinonin Lafiya na Najeriya ya ɗamfaru da shirin wajen magance matsalar, wanda gangami ne na ƙasa baki ɗaya da ke da ƙudirin yi wa ‘yan Najeriya miliyan goma gwajin hawan jini da ciwon siga a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya na Abuja, a tsawon mako guda.
Read Also:
Daga cikin manufofin shirin akwai yi wa al’ummar Najeriya miliyan goma gwajin hawan jini da ciwon siga, da haɗa sakamakon da aka tabbatar da hanyoyin samun waraka, da samar da magunguna na ƙaramin zango daidai da tsarin da ya dace, da ƙara wayar da kan al’umma da ilimantar da su game da hawan jini da ciwon siga, da ilimantar da al’umma game da abincin da za su rinƙa ci, da motsa jiki, da kaucewa shan taba, da sauransu.
Dakta Labaran ya buƙaci mutane da su shigo a dama da su a cikin wannan aiki don tabbatar da yadda matakin lafiyarsu yake, ya ƙara da cewa waɗanda aka samu da waɗannan cututtuka za a ba su magani kyauta ko kuma a tura su asibiti mafi kusa domin a ci gaba da kula da lafiyarsu idan an fahimci larurar tasa babba ce.
Kwamishinan ya shawarci jama’a da su kai iyalansu wuraren da aka ware don yin gwajin a cibiyoyin da aka tanada don yin aikin kyauta har tsawon mako guda a faɗin jihar Kano, yana mai fatan yi wa mutane miliyan ɗaya a ɗaukacin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.
Ya ce “Aikin, wanda zai lashe kusan Naira miliyan 800, babba ne. Saboda haka, mutane, daga kan ɗan shekara 20 zuwa sama, na buƙatar su yi cikakken amfani da wannan dama wajen yin gwajin waɗannan cututtuka masu hallakarwa. Waɗanda aka samu da ɗaya ko kuma duka cututtukan kada su razana, maimakon haka su gode wa Allah saboda an gano wata cuta da ta ɓuya a jikinsu, domin su nemi waraka.
Dakta Labaran ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake nuna damuwa da lafiyar al’ummar jihar Kano a kowane lokaci, ya kuma jinjina wa ƙungiyoyi masu tallafa wa fannin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki bisa yadda suke bayar da gudummawa wajen ci gaban lafiya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 21 minutes 53 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 3 minutes 18 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com