Manyan dillalan man fetur a Najeriya, sun tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa akwai wadattacen man fetur a ƙasar, don haka ‘yan ƙasar su kwantar da hankalinsu.
Read Also:
Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar manyan dillalan, Clement Isong, ya fitar ranar Laraba ya ce akwai wadattacen mai a rumbunan ajiyar matatar mai ta Dangote da na babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL.
Isong ya ƙara da cewa babu wata barazana game da ƙarancin man fetur a ƙasar.
A makon nan ne dai kamfanin mai na NNPCL ya ƙara farashin man fetur a ƙasar.
To sai dai duk da haka an riƙa ganin dogayen layuka a wasu gidajen man ƙasar, wani abu da ya ƙara haifar da fargabar ƙaruwar farashin man a zukatan ‘yan ƙasar.