Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarnin kammala ƙwace wasu kuɗi kimamin dala miliyan biyu daga wajen tsohon gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele.
Yayin da yake yanke hukuncin, alƙalin kotun mai shari’a, Dehinde Dipeolu ya kuma bayar da umarnin ƙwace wasu kadarori bakwai masu alaƙa da tsohon gwamnan na CBN, da kuwa wasu takardu mallakar hannayen jari.
Mai shari’a Dipeolu ya ba da umarnin ne bayan buƙatar hakan daga lauyoyin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC.
Kotun ta ƙwace kadarorin ne bayan da ta ce tsohon gwamnan na CBN ya kasa alaƙanta abin da ta kira ‘halastaccen samunsa’ a lokacin da yake aiki da bankin Zenith da kuma CBN da kuma mallakar kadarorin.
Haka kuma kotun ta ce mista Emefiele ya kasa gabatar da takardun da ke nuna cewa kadarorin mallakarsa ne.
A ranar 15 ga watan Agustan da ya gabata ne kotun ta bayar da umarnin wucin gadi ga EFCC na ƙwace kuɗin da suka kai dala miliyan 2.045 da kadarorin bakwai da takardun mallakar hannayen jarin bayan sauraron ƙarafin da lauyoyin hukumar suka gabatar mata.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 48 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 30 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com