Majalisar tattalin arzikin Najeriya NEC ta shawarci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya janye ƙudurin yi wa harajin VAT garambawul da ya aika majalisar dokokin ƙasa domin a samu isasshen lokacin da za a tattauna tare da fahimtar juna game da abin da ake nufi gyara VAT ɗin.
Tun da farko gwamnonin Arewa da sarakunan yankin sun yi zama na musamman a Kaduna tare da wasu masu ruwa da tsaki a yankin, inda suka yi fatali da ƙudirin na shugaban ƙasa.
Majalisar ta bayyana hakan ne bayan zamanta na 145 a ƙarƙashin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a Abuja.
Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan shugaban kwamitin shugaban ƙasa na musamman kan tsare-tsare da yi wa haraji garambawul, Mista Taiwo Oyedele ya gabatar da jawabi game da tsare-tsaren da suke yi, inda majalisar ta ce akwai buƙatar a samu ƙarin lokaci domin tattaunawa tare da fahimtar juna.
Haka kuma Kashim Shettima ya ce za su ɗauki matakai da suka dace domin tabbatar da ba a sake samun irin katsewar lantarkin da aka fuskanta ba a kwanankin baya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 21 minutes 6 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 2 minutes 31 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com