Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana mutuwar shugaban rundunar sojin Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, wanda ya mutu yana da shekaru 56 a duniya.
Wannan na cikin wata sanarwa da masawarci na musamman ga shugaban kasar kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fita, aka raba manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa Taoreed Abiodun Lagbaja ya mutu a daren talata bayan fama da rashin lafiya.
An haifi Taoreed Lagbaja a 28 ga watan Fabrerun 1968, sannan shugaban kasa Asiwajo Bola Ahmad ya nadashi matsayin Hafsan sojojin Najeriya a ranar 19 ga watan Yunin 2023.
ya fara aiki da rundunar sojin kasar ne bayan daukar horo a kwalejin sojojin kasar ta Nigerian Defence Academy a 1987, in da a ranar 19 ga watan satumba 1992, ya fito a matsayin Second Lieutenant rukuni na 39 (39th Regular Course).
Read Also:
a yayin aikinsa Lt. General Lagbaja ya nuna gogewa da shugabanci na gari gami da sadaukar a matsayin kwamandan bataliya ta 72 rukunin sojoji na musamman.
ya kuma taimaka matuka wajen gudanar da ayyukan tsaron cikin gida, wanda ya hadar da jagarantar dakarun OPERATION ZAKI a jihar Benue, Lafiya Dole a jihar Borno, Udoka a kudancin Nijeriya, da Operation Forest Sanity a yankin Jihohin Kaduna da Niger.
haka kuma ya halarci kwalejin sojoji ta Amurka in da ya yi sami digiri na II a dabaru wato “Strategic Studies” wanda hakan ya bashi damar nuna sadaukarwa da kwarewa gami na son cigaban harkokin shugabancia a ayyukan soji.
Lt. General Lagbaja yana da Mata daya Mai suna Mariya da ‘ya’ya guda biyu.
daga bisani shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da rundunar sojin Nijeriya bisa wannan rashi ya kuma yi masa addu’a da kasa baki daya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 56 minutes 1 second,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 37 minutes 26 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com