Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya ce ba ya yi wa Tinubu hassada, inda ya ce ya jefa ƴan Najeriya cikin kunci.
Ɗan takarar shugaban ƙasar karkashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, na mayar da martani kan kalamai da fadar shugaban Najeriyar ta yi cewa yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na shugaban ƙasa.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar ranar Lahadi, ya soki Atiku kan ci gaba da sukar tsare-tsaren tattalin arzikin da shugaban, maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam’iyyarsa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar dai ya sha sukar tsare-tsare da gwamnatin Tinubu ta ɓullo da su, musamman na tattalin arziki, inda ya ce babu abin da za su haifar illa jefa ƴan Najeriya cikin kunci da wahala.
Wata sanarwa da mai taimakawa Atiku na musamman kan yaɗa labarai Phrank Shaibu ya fitar ranar Litinin, Atiku ya ce sai Tinubu ya aiwatar da tsare-tsare kafin yake duba illolin da za su haifar.
“Tinubu bai shiryawa mulki ba. Sai ya aiwatar da abu kafin yake duba illarsa daga baya. Wannan shi ya sa ya sanar da janye tallafin man fetur ba tare da kawo abin da zai rage wa ƴan ƙasar raɗaɗi ba.
“Abin mamaki ne a yi iƙirarin cewa Atiku na kyashin Tinubu. Ba zai yi hassada da Tinubu ba saboda irin kunci da ya jefa ƴan Najeriya,” in ji sanarwar.
Atiku ya ce babu wani adalin shugaba wanda yake da zimmar ganin ƴan Najeriya cikin walwala da zai yi hassada da irin gallazawa da ake yi musu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1245 days 13 hours 56 minutes 48 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1227 days 15 hours 38 minutes 13 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com