Hukumar Dake Hana Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi Ta Kasa NDLEA Reshen Jihar Kano ta Bayyana Cewa ta Samu Tarin Nasarori a Kokarin ta na Yaki da Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi a Jihar ta Kano
Hukumar Ta Cikin Wata Sanarwa da kakakin ta Sadik Muhammad Maigatari Ya aikewa manema labarai tace, a Watan Jiya Bayan Gurfanar da Wasu da Hukumar ta Kama, Kotu ta Yanke wa Wasu Mutane 22 Hukunci a Gidan Gyaran hali da Tarbiyya
Read Also:
A cewar Sanarwar Wannan Yana daga Kokarin Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi NDLEA ta Jihar Kano Karkashin jagorancin CN. AI Ahmad Wanda Yake aiki tukuru Wajen Kawar da Shan Miyagun kwayoyi a Jihar Kano
Hukumar ta NDLEA tace Zata Cigaba da Tabbatar da kawar da dabi’ar Shaye Shayen Miyagun kwayoyi a Tsakanin Al’ummar Jihar Kano.
Hukumar ta Kuma Godewa Al’ummar Jihar Kano da Gwamnatin jihar ta Kano harma da alkalai Bisa Hadin Kai da Suke baiwa Hukumar Wajen Gudanar da Ayyukan ta.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1246 days 2 hours 44 minutes 52 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1228 days 4 hours 26 minutes 17 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com