Home General Sojoji sun shirya yadda za a yi maganin mayaƙan Lakurawa – Badaru

Sojoji sun shirya yadda za a yi maganin mayaƙan Lakurawa – Badaru

Nigerian Army

Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun kammala shirye-shiryen murƙushe ‘yan ƙungiyar Lakurawa, masu iƙirarin jihadi da ke addabar jama’a a waɗansu jihohin arewa maso yammacin kasar.

Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan ƙungiyar suka kai hari a makon daya wuce a jihar Kebbi inda suka hallaka mutum 15 tare da jikkata wasu da dama.

Ministan tsaro na Najeriya, Muhammadu Badaru Abubakar ne ya bayyana ƙudurin rundunonin sojin ƙasar na tunkarar matsalar tsaron ta Lakurawa da ta kunno kai kwanannan,

Ministan ya ce manyan hafososhin tsaron Najeriya sun riga sun fitar da wani tsari na musamman da zai hana ‘yan Lakurawan yin tasiri a arewacin kasar.

Ya ƙara da cewa manyan hafsoshin rundunonin sojin ƙasa da na ruwa da na sama sun gana da hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa, inda suka yi masa bayani kan matakan da suka shirya ɗauka kan wannan ƙungiya.

“Ni ma sun yi mani bayani kuma na gamsu da shirinsu. Idan Allah ya yarda za a samu nasara nan da ɗan lokaci ,” in ji ministan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp