Kamfanin Dangote ya sanar da rage farashin tacaccen man fetur din da yake sayarwa dillalan man a Najeriya.
Mai magana da yawun kamfanin Anthony Chiejina yace sun rage farashin ne daga naira 990 kowacce lita zuwa naira 970 domin saukakawa jama’ar Najeriya.
Read Also:
Sanarwar ta ce kamfanin na Dangote ya dauki wannan matakin ne domin nuna godiya ga ‘yan Nijeriya bisa goyon bayan da suke ba Dangote.
Idan za a iya tunawa kamfanin Ɗangote ya Fara sayar da man matatarsa ne akan farashin Naira 990 ga dillalai, sai dai yasa fama da kalubale daga bangarori daban-daban.