Matatar man fetur ta Fatakwal da ke jihar Rivers ta dawo aiki, inda ta fara tace man fetur, kamar yadda babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin NNPCL, Femi Soneye ya bayyana.
A cewarsa, “yau an samu wata gagarumar nasara domin matatar man fetur ta Fatakwal ta fara tace man fetur.
Read Also:
Wannan wani sabon babi ne a ɓangaren makamashi a Najeriya, da yunƙurin inganta tattalin arzikin ƙasar,” kamar yadda ya bayyana a ranar Talata.
Ya ce za a fara lodin man fetur ɗin a yau Talata, sannan ya ƙara da cewa kamfanin na NNPCL na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da ita ma matatar Warri ta fara aiki, kamar yadda shafin intanet na tashar Chanells ya ruwaito.