Gwamnatin jihar Kano Ta Dawowa Da Jami’ar Yusuf Maitama University sunanta na Asali wato Northwest University.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano Dr. Yusuf Kofar mata ya wallafa a shafinsa na facebook.
Ya ce, a zaman majalisar zartarwar jihar kano na 21 da ya gudana karkashin jagorancin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, majalisar ta amince da maidawa da jami’ar sunanta na asalai wato NORHTWEST UNIVERSITY, KANO
Read Also:
Kazalika majasar zartarwar ta amince a sanya sunan na Yusuf Maitama Sule a abuwar kolejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari domin girmamawa ga mai sunan.
Kofarmata ya kuma bayyana cewa tuni aka bayar da umarnin tura waɗannan kuduri zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano domin zamar da su doka, ciki harda gyaran dokar shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 22 hours 51 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 33 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com