Shalkwatar tsaron Najeriya ta yi martana kan rahoton Amnesty

Shalkwatar tsaron Najeriya ta musanta zargin da ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty International, ta yi cewa mutum 10,000 ne suka mutu a hannun sojojin, tun bayan ɓarkewa rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Daraktan ƙungiyar Amnesty a Najeriya, Mallam Isa Sanusi ne bayyana zargin sojojin da hannu a mutuwar mutanen da sauran nau’ikan cin zarafi, a wani jawabi da ya yi a tarin manema labarai a birnin Maiduguri.

Isa Sanusi a ce tuni ƙungiyarsu ta shigar da ƙara gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague kan zarge-zarge take haƙƙin ɗan’adam da take yi wa sojojin a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

To sai dai yayin da take mayar da martani shalkwatar tsaron ƙasar, cikin wata sanarwa da kakakinta, Manjo Janar Edward Buba ya fitar ranar Juma’a ya bayyana zarge-zargen da masu tayar da hankali, kuma marasa tushe, kuma marasa hujja’.

”Duk da cewa yaƙin da sojoji ke yi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya mai sarƙaƙiya ne cike da ƙalubale, muna bin ƙa’idojin da suka kamata. A duk lokacin da muka kama waɗanda ake zargi bayan ɗaukar bayanansu, mukan miƙa su hannun hukumomin da ya kamata domin a sake su ko a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Manjo Janar Edward Buba.

Sanarwar ta kuma ce shalkwatar tsaron ta gayyaci ƙungiyar ta Amesty zuwa ofishinta domin tabbatar da zarge-zargen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com