Babban kamfanin mai na Najeriya NNPCL na gudanar da jarrabawar ɗaukar sabbin ma’aikata.
Cikin wani saƙo da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce kimanin mutum 45,689 ne suke gudanar da jarrabawar wadda aka yi da kwamfuta.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
”A yau NNPCL ya fara gudanar da jarrabawar ɗaukar ma’aikata da ake gudanarwa ta hanyar kwamfuta a cibiyoyi da dama a faɗin ƙasar nan”, in ji sanarwar.
NNPCL ya bayyana tsarin ɗaukar ma’aikatan da cewa tsari ne da yake gudanarwa a bayyane domin bai wa kowa dama.
”Domin damawa a kowa wajen ɗaukar aiki, NNPCL ya yi tanadi na musamman domin tabbatar da masu lalurar buƙata ta musamman da ke cikin masu neman aikin, sun samu damar gudanar da jarrabawar ba tare da wata matsala ba”, kamar yadda kamfanin ya wallafa a shafinsa na X











