Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya taya ɗan takarar shugaban ƙasar Ghana na jam’iyyar NDC mai hamayya, John Dramani Mahama, murnar nasarar da ya samu a zaɓen ƙasar.
Wannan na zuwa ne bayan da mataimakin shugaban ƙasa Muhammadu Bawumia ya amince da shan kaye.
Read Also:
Wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce shugaba Tinubu ya yi fatan cewa hulɗa tsakanin ƙasashen biyu za ta ƙaru da kuma ganin kwanciyar hankali a faɗin ƙasashen ƙungiyar Ecowas.
Tinubu ya jinjinawa ƴan Ghana ta yadda suka fito suka yi zaɓe, inda a ɗaya gefen ya kuma yaba wa halin dattako da Bawumia ya nuna na amsa shan kaye tun kafin hukumar zaɓen Ghana ta sanar da sakamakon.
Har yanzu dai hukumar zaɓen ƙasar ba ta fara bayyana sakamakon zaɓen a hukumance ba.