Home General Babu wata karamar hukumar dake hannun boko haram – Gwamnatin Borno

Babu wata karamar hukumar dake hannun boko haram – Gwamnatin Borno

Gwamnatin Jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya ta ce mayakan boko haram sama da dubu 170 suka ajiye makamansu a karkashin shirin afuwar da ta bullo da shi da zummar kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe shekaru 14 ana yi a jihar.

Kwamishinan yada labarai Farfesa Usman Tar ya bayyana haka dangane da tashin hankalin da ya yi sanadiyar rasa dubban mutane da kuma raba sama da miliyan 2 da muhallinsu lokacin da ya ziyarci RFI Hausa.

Farfesa Tar yace shirin na su na afuwa da suka yiwa suna ‘Borno model for peace, reconciliation and development’ ya taimaka wajen haifar da zaman lafiya a sassan jihar.

Kwamishinan ya ce tun shekarar 2021 da Abubakar Shekau ya kashe kansa, gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum ya kira taron jama’ar jihar wanda ya goyi bayan matakan da gwamnati ke dauka na tabbatar da zaman lafiya da kuma aiwatar da shirin afuwar.

Tar ya ce a karkashin shirin an umarci duk wani ‘dan bindiga da yake bukatar aje makaminsa da ya kai kansa wurin sojoji wadanda daga bisani zasu tantance shi tare da mikawa jami’an gwamnati wadanda ke aiwatar da shirin sulhun bayan kwance musu damara.

Kwamishinan yace shirin ya samu karbuwa sosai ganin yawan mayakan da suka aje makamansu, aka kuma horar da su wajen sauya musu tunani tare da sanya su cikin jama’a.

Tuni wannan shiri ya samu goyan bayan Majalisar dikin duniya lokacin da Sakatare Janar Antonio Guterres ya ziyarci Maiduguri domin ganewa idansa irin matakan da gwamnatin jihar ke dauka na magance matsalar da ake fuskanta.

Farfesa Tar ya ce a halin yanzu an samu karuwar ayyukan noman da akeyi a jihar wanda yake taimakawa jama’a wajen samun abincin da ake nomawa la’akari da cewar akasarin mutanen jihar manoma ne.

Jami’in yace an samu karuwar ayyukan gona sosai a wannan daminar da ta gabata, yayin da kuma yanzu jama’s suka rungumi noman rani tare da samun tallafin gwamnatin jihar.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewar babu gaskiya a labarin da wasu ke yi cewar har yanzu a kwai wasu kananan hukumomin dake karkashin ikon boko haram a fadin jihar, saboda jajircewar da sojoji keyi da kuma shirin da gwamnatin jihar ke yi.

Dangane da shirin mayar da mutane garuruwansu kuwa, Farfesa Tar yace aikin ya yi nisa sosai, la’akari da yawan jama’ar da aka mayar garuruwansu bayan sake gina musu gidaje da makarantu da kuma asibitoci, yayin da ya kara da cewa ko a wannan watan a kwai wasu da dama da za’a mayar garuruwan na su.

Kwamishinan ya yi watsi da masu zargin cewar ana tilastawa mutane komawa garuruwan na su ba tare da samun tsaron da ake bukata ba, ya yin da yace bayan sake gina garuruwan sai jami’an tsaro sun tabbatar da zaman lafiyar yankunan kafin a kai mutane.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp