Babban bankin Najeriya CBN ya taƙaita hada-hadar kuɗin da masu PoS za su yi a rana zuwa naira miliyan 1.2.
Wannan umarnin na ƙunshi ne a cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Talata game da taƙaita hada-hadar kuɗi ga wakilan bankuna.
“Bankin ya ɗauki wannan matakin ne domin ƙara jawo hankalin masu hada-hadar kuɗi zuwa ga rage amfani da tsabar kuɗi,” kamar yadda sanarwar, wadda Oladimeji Yisa Taiwo ya sa hannu a madadin daraktan tsare-tsaren fitar da kuɗi.
Zuwa watan Yulin 2024, akwai masu PoS miliyan 3.05 da suke hada-hada, sannan masu PoS da suka yi rajista sun kai miliyan 4.06 kamar yadda tashar Channels ta kalato daga shafin Nigeria Interbank Settlement System Plc.