Asusun ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF, ya ce Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya waɗanda yaran da ke ƙasar ba sa zuwa makaranta.
Al’amarin da galibi yawan rikice-rikice da rashin tsaro suka haifar a sassa da dama na ƙasar.
A sakamakon haka, wata mata ta sami karsashin kafa gidauniyar ilimi a wani ƙauye na jihar Filato, bayan da iyalai da dama suka kasa biyan kudaden makarantar yaransu.
Da gidauniyar ce take wayar da kai tare da taimakon yara suna zuwa makaranta.