Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya ce koma-baya da ake samu a yankin Arewa laifi ne na jagororin siyasar yankin.
Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su goya wa Tinubu baya kan yunƙurinsa na inganta tattalin arzikin ƙasar ta hanyar ƙudurorin haraji.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Dogara ya bayyana hakan ne a wani taron jagororin kiristoci ƴan arewacin Najeriya, inda ya ce jagororin yankin ba su yi amfani da damar da suka ba na kusan shekara 40, wanda hakan a cewarsa ya jefa yankin talauci da rashin aikin yi.
“Ba Tinubu ko yankin kudu ba ne matsalarmu. Wasu na ƙorafin cewa Yarbawa suna samun muƙamai da yawa, amma kar mu manta, mun yi mulkin sama da shekara 40. Me za mu nuna? har yanzu arewa na nan yadda take,” in ji shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.











