Gwamnatin Najeriya ta ba da hutun bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara

Gwamnatin tarayya ta bayar da hutun aiki a ranar Laraba 25 da Alhamis 26 ga watan Disamban 2024 domin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da babban sakatariyar ma’aikatan, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Litinin.

Tunji-Ojo ya miƙa gaisuwarsa ga ƴan Najeriya, sannan ya yi kira gare su yi amfani da lokacin bukuwan domin nuna ƙauna da kira ga zaman lafiya.

Ya ce gwamnatin Najeriya a shirye take ta cigaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ci gaban ƙasar, sannan ya taya kiristoci murna, tare da musu fatan alheri.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com