Yadda Gwamnan Adamawa ya kirkiri sabbin Masarautu bakwai a jihar

Gwamnan Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, Ahmadu Umaru Fintiri ya sanar da ƙirƙiro sabbin masarautu bakwai a jihar.

Sabbin masarutun sun haɗa da masarautar Huba da ke Hong, da masarautar Madagali da ke Gulak, da masarautar Michika da ke Michika da masarautar Fufore da ke Fufore da masarautar Gombi da ke Gombi, da masarautar Yungur da ke Dumne, sai kuma masarautar Maiha da ke Maiha.

A cewar gwamnan, masarautar Huba da Madagali da Michika da kuma Fufore na da matakin girma na biyu, yayin da masarautun Gombi da na Yungur da kuma na Maiha an basu matakin girma na uku.

”ƙirƙiro waɗannan sabbin masarautun na da nufin inganta matsayin masarautu wajen samar da zaman lafiya da tsaro da kuma cigaban jihar,” a cewar gwamnan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com