Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya ta PDP ta ce za su samu ƙarin gwamnoni a zaɓen 2027, ƙari a kan guda 12 da take da su a yanzu, sannan ta karɓe mulkin ƙasar.
Jagororin jam’iyyar ne suka bayyaka haka a lokacin da suka kai ziyara ga Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, kamar yadda tashar Channels ta wallafa a shafin ta.
Ma’ajin jam’iyyar, Alhaji Ahmed Yayare ne bayyana hakan a madadin jam’iyyar, inda ya ce yanayin yadda ƙasar ke fama da taɓarɓarewar tattalin arziki ne ya sa PDP za ta samu sauƙin samun nasara a 2027.
Ya ƙara da cewa, “babu abin da zai hana PDP karɓe mulkin ƙasar. Yanzu APC ba ta abin da za ta yi kamfe da shi saboda yunwa da talauci ya yi a ƙasar. Idan suka fita kamfe sai an jefe su.”