Rundunar ‘yansandan Najeriya ta ce wani abin fashewa ya kashe mutum biyu a makarantar Islamiyya da ke Abuja babban binrin ƙasar.
Wata sanarwa da rundundar ta wallafa ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Litinin a ƙauyen Kuchibuyi da ke ƙaramar hukumar Bwari.
“Bayanan farko-farko sun nuna wasu mutum uku ne suka kai wa shugaban makarantar Tsangayar Sani Uthman Islamiyya Mallam Adamu Ashimu ziyara, kuma su ake zargi da kai bam ɗin,” in ji sanarwar.
“Biyu daga cikin mutanen sun mutu a fashewar a farfajiyar makarantar, yayin da na ukun da kuma wata mata mai sayar da kayayyaki suka ji munanan raunika kuma suke samun kulawa a asibiti.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ‘yansanda na tsare da Mallam Adamu, sannan kuma za ta bayyana abin da bincikenta ya gano.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 2 hours 16 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 3 hours 58 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com