Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce nahiyar Afirka na da duk abin da ake buƙata domin riƙe kanta da kanta.
Tinubu ya bayyana haka ne a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a ranar Litinin lokacin da yake ganawa da Shugaban Ƙasar Rwanda, Paul Kagame.
Tinubu ya wallafa a shafinsa na X cewa, “a yammacin yau a makon taron ci gaba na Abu Dhabi, na samu ganawa da Shugaban Ƙasar Rwanda, Paul Kagame.
“Nahiyar Afirka na da duk abin da ake buƙata domin ciyar da kanta gaba. Muna da ɗimbin arziki da mutane da ƙwarewa. Dole mu yi nazari a tsakaninmu domin inganta hanyoyin kasuwancin ƙasashen Afirka domin amfanin nahiyarmu da mutane. Yanzu ne lokacin da Afrka za ta dara.”
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 14 hours 39 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 16 hours 20 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com