Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya ce ya zuwa watan Satumban shekarar 2024, kuɗin da ya samar wa gwamnatin tarayya ya kai naira tiriliyan 100.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya sanar da hakan a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin kuɗi na majalisar dattawa, inda yake kare kasafin kuɗin kamfanin na bana.
Ya ce NNPCL na fitar da bayanan asusunsa na shekara-shekara, “Hada-hadarmu a fili suke, kuma muna bayyana duk harkokin kuɗin da muka yi a fili ba tare da nuƙu-nuƙu ba,” in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Kyari ya ce kamfanin na NNPCL ne kamfanin da ya fi biyan haraji, kuma wanda ya fi samar da riba ga masu zuba jari.
Sai dai ya ce sai sun zauna tare da daraktocin kamfanin ne za su iya fitar da hasashen kuɗin da za su samar a bana.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 16 hours 28 minutes 45 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 18 hours 10 minutes 10 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com