Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya (NLC), ta yi kira ga Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu da ya sauka daga mukaminsa saboda yawaitar katsewar babban layin lantarki na ƙasa.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero ya fitar, ya ce ƙungiyar na takaicin yadda ɓangaren lantarkin Najeriya ya ƙi gyaruwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Read Also:
A cewar Ajaero, “Idan har akwai ma’aikata ƙwararru waɗanda suka san makamar aiki a ma’aikatar makamashi, to lallai za’a iya kiyaye yawaitar abin kunyar nan da ake fuskanta na yawaitar katsewar layin lantarki a Najeriya. Magance matsalar ya kamata ministan ya yi, ba ya riƙa maganar cewa za su magance ta ba.
“Mun yi amannar cewa wannan ya nuna rashin ƙwarewa da gazawar ma’aikatar makamashin, wanda hakan ya sa muke mamakin me ya sa wanda ke jagorantar ma’aikatar ba zai sauka cikin mutunci ba”.
A karshe Ajaero ya kuma caccaki ministan bisa kasafta kashe naira biliyan 8 a kasafin kuɗin 2025 domin “wayar da kan ƴan Najeriya muhimmancin biyan kuɗin lantarki.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1488 days 56 minutes 37 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1470 days 2 hours 38 minutes 2 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com