Majalisar dokokin jihar kano ta yiwa dokar samar da jami’an tsaron jiha karatu na biyu a zauren majalisar domin tabbatar da ingata harkokin tsaro.
Dokar wanda shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa ya karanto ya tsallake karatu na biyu a zaman majalisar.
Read Also:
Dokar idan ta tabbata zata samar ‘yan sandan jihohi kamar dai yadda wasu jihohi a kudancin kasar suka a samar irinsu Amotekun, kuma za’a basu damar kama duk wanda aka samu da laifi ko waye shi idan yana cikin jihar Kano.
wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da wasu jihohi a arewa maso yammacin kasar ke fama da matsalar rashin tsaro da taki ci taki cinyewa