Hukumar Kula da Zirga- zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA ta musanta jita-jitar da ake yadawa na fara daukar aiki a Hukumar.
Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a ranar lahadi, ta bakin mai magana da yawun Hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa inda Yace Babu gaskiya a batun daukar Sabbin Ma’aikata.
Nabilusi Kofar Na’isa Ya ce Hukumar ta lura da jita-jitar da ake yadawa na fara daukar sabbin Jami’an Hukumar wadanda hakan ba gaskiya ba ne kwata-kwata.
Read Also:
Sai dai Kuma sanarwar tace Hukumar na tsaka da aikin tantance daukacin Jami’an KAROTA domin duba yuiwuwar daukar sabbi.
A don haka Hukumar ke gargadin jama’a, da su guji yada jita-jitar fara daukar sabbin Jami’an na Hukumar ta KAROTA
Hukumar ta ce duk wanda ta kama da hannu wajen yada jita-jitar zata dauki matakin sharia a kansa.
Engr. Faisal ya roki jama’a da su yi gaggawar sanar da Hukumar ta KAROTA ko ofishin ‘Yansanda mafi kusa wanda duk aka samu yana yada jita-jitar