Matatar mai ta Dangote ta bayyana cewa ta rage farashin man daga Naira N890 zuwa Naira N825 duk lita
Read Also:
Wannan na cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar inda ya ce ya rage farashin man ne sakamakon karatowar watan azumin Ramadan, don tallafawa yunkurin shugaban kasa na sasauta al’amura a Nijeriya.
Wannan ne dai karo na biyu a watan fabarairu da Dangote ya rage farashin man fetur bayan karin da aka samu kwanakin baya.
Sanarwar ta ce Sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 27th February 2025.