Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta rufe wasu hanyoyin ne da suke dangana mutane da gidan sarki na Nasarawa dake kan titin zuwa gidan gwamnati saboda bayanan sirri da suka samu na kokarin kawo hargitsi a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar laraba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce “A sakamakon wadannan matakan da aka dauka, an kama wasu mutane 17 da ake zargi da aikata laifuka, kuma ana ci gaba da bincike. Rundunar zata tabbatar ta gurfanar da wadanda ake zargi da aikata wannan tashin hankali a gaban kuliya.
Rundunar ta gargadin daidaikun mutane da kungiyoyi game da yin duk wani nau’i na taro, jerin gwano, bisa ka’ida ba. Kaucewa Wannan gargadi zai iya sawa jami’an tsaro su dauki mataki.
Kiyawa ya yi kira ga jama’a da su sanya ido tare da kai rahoto ga jami’an tsaro na duk wani abu da ba su aminta da shi ba, haka kuma Rundunar ta yaba da hadin kai da goyon bayan mutanen jihar Kano ke ba ta a kokarinsu na wanzar da zaman lafiya.











