Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar juma’a 28 ga watan Fabrairun 2025, a matsayin ranar hutun Zango karatu na biyu ga makarantun firamare da sakandire dake faɗin jihar.
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ce ta sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar Balarabe Abdullahi Kiru ya rabawa manema labarai, inda ya ce hutun ya shafi makarantu masu zaman kansu da kuma na gwamnati.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ce daliban makarantun firamare da sakandire na kwana za su koma Makarantunsu a ranar lahadi 06 ga watan Afirilun 2025, a yayin da su kuma na makarantun jeka ka dawo za su koma Makarantar a ranar litinin 07 ga watan Afirilu, 2025.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano Dakta Ali Haruna Makoda, ya buƙaci iyayen yaran da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma Makarantar a ranakun da aka sanya.
A ƙarshe sanarwar ta gargaɗi dukkan makarantu masu zaman kansu da su tabbatar da bin ƙa’idar da aka gindaya ko kuma su fuskanci hukunci.











