Gwamman jihar kano engr abba kabir yusuf, Ya amince da kafa kwamitin da zai bincike dalilin da yasa aka yankewa wasu daga cikin Ma’aikatan jihar kano a wannan wata da Muke ciki.
Cikin wata sanarwa da darktan Yada Labarai na Gwamann Sunusi bature dawakin Tofa ya fitar aka rabawa Manema Labarai yace, gwamman ya nuna damuwarsa da samun Labarin wanda hakan yasa ya kafa kwamitin.
Sakataren gwamnantin jihar kano Ahaji Umar Faruk Ibrahim shine ya kaddamar yan kwamitin a ofishinsa a yau alhamis.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
An baiwa kwamitin wa’adin kwanaki 7 domin gabatar da rahotonsa akan wanann matsala da aka samu domin ya gano ko tangardar na’ura ce ko kuma zagon kasa ne da ake kokarin yiwa gwamnantin jihar kano domin Daukar mataki
Kwamitin zai kasance karkashin. Hon. Abdulkadir Abdussalam – Chairman wanda shine kwamishinan raya karkara da raya birane.
Dr. Bashir Abdu Muzakkari
Dr. Aliyu Isa Aliyu
4. Dr. Hamisu Sadi Ali
6. Aliyu Muhammad Sani
7. Ummulkulthum Ladan Kailani
Mikiya Hausa Times ta rawaito cewa wasu Ma’aikatan jihar kano ne suka koka da cewa an yanke musu albashi na wannan wata da muke ciki kamar yadda rahotanni suka bayyana.











