Natasha ta zargi Akpabio da Neman lalata da ita

Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a zauren Majalisar dattijan Nijeriya Natasha Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio, da neman yin lalata da ita.

Natasha, tace kin amincewar data yiwa Akpabio ya yi lalata ta shine dalilin da yasa ake samun tankiya tsakanin ta dashi.

Akpoti, ta yi wannan zargin yayin wata hira da talbijin ta Arise a yau Juma’a.

A makon daya gabata ne aka samu rashin jituwa tsakanin Akpabio da Natasha, a zauren majalisar wanda hakan ya janyo cece-kuce da hatsaniya a zauren majalisar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com