Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin kasafin kudin 2025 na kimanin Naira Tiriliyan 54.99 ya zama doka.
Read Also:
Majalisar tarayya ce ta zartar da kudirin a ranar 13 ga watan Fabrairun 2025, bayan da aka kara akan naira tiriliyan 49.7 da shugaba Tinubu ya gabatar.
An rattaba hannu kan kasafin kudin ne yayin wani kwarya-kwaryan biki a ofishin shugaban kasa, a yau Juma’a.
Dokar Kasafin Kudi ta 2025 ta samu karin kashi 99.96% daga kasafin kudin 2024 na Naira tiriliyan 27.5.