Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar Namibia, Dr. Sam Nujoma.
Tinubu wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta a wajen jana’izar ban girman da aka yi wa marigarin ya bayyana shi a matsayin jarumin da ya ƙarfafa wa ƙasashen Afirka gwiwa wajen neman ƴancin kansu.
Yayin da yake jawabi a wajen jana’izar, Kashim Shettima ya ce ƙasashen Afirka ba za su manta irin gudunmawar da Mista Nujoma ya ba su wajen tabbatar da ƴancin kawunansu ba.
Najoma wanda shi ne shugaban Namibia na farko – ya rasu ne a ranar 8 ga watan Fabrairu, yana da shekara 95 a duniya, bayan fama da jinya a wani asibiti a Windhoek, babban birnin ƙasar.