PSC ta amince da Nadin CP Ibrahim Adamu Bakori matsayin kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano

Hukumar kula da aikin Ƴansanda ta Najeriya (PSC), ta amince da naɗa CP Ibrahim Adamu Bakori, a matsayin sabon kwamishinan ƴansandan jihar Kano.

Shugaban hukumar, DIG Hashimu Argungu mai ritaya ne ya tabbatar da naɗin inda ya nemi sabon kwamishinan da ya tabbatar da an samu zaman lafiya mai ɗorewa a jihar, ta hanyar tunkarar ƙalubalen da ke gabansa wajen tabbatar da an daƙile ƙaruwar aikata laifuka a jihar mai yawan jama’a.

CP Bakori dai zai maye gurbin CP Salman Garba Dogo ne biyo bayan samun ƙarin girma zuwa mataimakin babban sifeto na ƙasa (AIG), kamar yadda sashen Hausa na BBC ya rawaito.

Kafiin naɗin nasa, CP Bakori ya kasance kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen binciken kisan kai (Homicide) a shelkwatar ƴansandan ƙasar da ke Abuja.

Jihar Kano dai na fama da matsalolin dabanci da ƙwacen waya da sace-sace, baya ga na baya-bayan nan wato rikicin masarautar Kano da ya janyo al’umma suka sauya tunaninsu kan rundunar ƴansandan jihar.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1485 days 17 hours 48 minutes 23 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1467 days 19 hours 29 minutes 48 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com