Home General Ƙungiyar ECOWAS na bikin cika shekaru 50 da kafuwa

Ƙungiyar ECOWAS na bikin cika shekaru 50 da kafuwa

A wannan makon ne Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika ECOWAS, ke cika shekaru 50 da kafuwa.

Ita dai ƙungiya ECOWAS, shugabannin ƙasashen yankin 15 ne suka haɗu wajen samar da ita a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 1975 a birnin Lagos da ke tarayyar Najeriya, da zummar bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗin kai da kuma tsaro.

Shugabannin ƙasashen dai sun haɗa da Benin da Burkina Faso da Côte d’Ivoire da Gambia da Ghana da Guinea da Guinea-Bissau da Liberia da Mali da Mauritania da Niger da Nigeria da Senegal da Saliyo da kuma Togo, duk da cewa a shekarar 1977 ƙasar Cabe Verde ta shigo ƙungiyar amma kuma a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2000, Mauritania ta fice daga cikinta.

A shekarar 1990, aka samar da rundunar ECOMOG a ƙarƙasashin ECOWAS, don gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a wasu ƙasashe mambobinta, matakin da ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasan ƙasashen Liberia da Saliyo.

To sai dai juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar a shekarun

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp