Rahotanni daga jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cewa kimanin mutum 20 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ƴan bindiga suka kai a wasu garuruwa biyu a jiya Lahadi.
Lamarin ya faru ne a yankin karamar Hukumar Augie – ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani.
Koda yake kawo yanzu ba a tabbatar ko su wa ne maharan ba.
Wani ɗan jarida Jameel Gulma dake a yankin ya bibiyi labarin, inda ya ce maharan sun kashe mutum shida ne, suka kwashe shanu, sai ƴan sa-kai suka bi su.
“A nan suka yi wa ƴan sa-kan kwantan ɓauna, suka buɗe musu wuta, inda suka kashe guda 13 daga cikinsu.”
jihar ta Kebbi na guda cikin jihohin arewacin Nijeriya dake fama da matsalar rashin tsaro, musamman na ‘yan bindiga dake satar mutane domin karbar kudin fansa wanda ke sake jifa jihar cikin halin na durkushewar tattalin arziki.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 22 hours 23 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 4 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com