Tinubu zai gana da shugabannin tsaro a Najeriya

Rahotanni a Najeriya na nuna cewa, shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na shirin yin wata ganawa da hafsoshin tsaron ƙasar kan kashe-kashe a jihohin Filato da Benue da wasu sassan ƙasar.

Ganawar na zuwa ne bayan komawar shugaba Tinubu Najeriyar, bayan kwashe makonni biyu yana ziyarar aiki a Paris, babban birnin Faransa.

Ana sa ran ganawar za ta sake duba ƙarin tashin hankalin da ake samu da kuma matakan magance su.

Hakan na zuwa ne a yayin da gwamnatin ƙasar ke ɗora laifin ƙarin kashe-kashen da ake samu a kan gwamnonin jihohi.

Gwamnatin tarayyar na ɗora alhakin hakan kan rashin sanya kuɗaɗe kamar yadda ya kamata a cibiyoyin tsaron da ke jihohi duk da ɗumbin kuɗaɗen da ake warewa domin yin hakan.

Matsalar tsaro na ci gaba da zama babban ƙalubale ga hukumomin tsaro a ƙasar, lamarin da ke sanadiyyar mutuwar dubban rayuka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com