Home General Akwai ƴanƙasar waje da ke kai hari a Benue – Hyacinth Alia

Akwai ƴanƙasar waje da ke kai hari a Benue – Hyacinth Alia

'Yan Ta'adda

Gwamnan jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya, Hyacinth Alia ya yi zargi cewa maharan da suka kai hari jihar ba ƴan Najeriya ba ne.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a wani shirin gidan talabijin na Channels, inda ya ce maharan na magana ne da wata irin Hausa da Fulatanci wanda ba irinsu ake yi a ƙasar ba.

“Waɗannan mutanen sun zo ne a shirye da makamansu da bindigogi ƙirar AK-47 da 49. Kuma ba su yi kama da ƴan Najeriya ba, ba sa magana kamar yadda muke yi, Hausarsu ba irin ta mu ba ce. “

Inda ya ƙara da cewa daga bayanan sirrin da suka samu daga mazauna yankunan da aka kai hare-hare, ya nuna cewa maharan ƴanƙsar waje ne.

Hakan na zuwa ne bayan wata ziyarar nuna alhini da mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya kai jihar.

Inda ya bai wa al’umomin jihar tabbataci kan matakan da ya ce gwamnatin na ɗauka domin magance matsalar tsaro a ƙasar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake zargin wasu ƙungiyoyin ƴanbindiga na ƙasashen waje na kai hari wasu sassan ƙasar.

Kamar ƙungiyar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sokoto da Zamfara da ke arewa-maso-yammacin ƙasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp